10 Nuwamba 2025 - 08:41
Source: ABNA24
Yemen Ta Gargaɗi Isra’ila: Duk Wani Sabon Hari Da Zata Kai Gaza Za Ta Fuskanci Martani Mai Tsanani

A cikin wani sako, Kwamandan Sojojin Yemen ya yi gargadin cewa idan gwamnatin Sahayoniya ta sake kai wani hari a yankin Gaza, ayyukan sojojin Yemen za su kai ga yankunan da aka mamaye.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Kwamandan Sojojin Yemen ya yi gargadin a cikin wani sako cewa idan gwamnatin Sahayoniya ta sake kai wani hari a yankin Gaza, ayyukan sojojin Yemen za su kai ga yankunan da aka mamaye.

A cikin wani sako, Kwamandan Sojojin Yemen ya yi gargadin cewa idan gwamnatin Sahayoniya ta sake kai wani hari a yankin Gaza, ayyukan sojojin Yemen za su kai ga yankunan da aka mamaye, kuma za a sake sanya haramcin zirga-zirgar jiragen ruwa na Isra'ila a cikin Tekun Bahrimaliya da Tekun Larabawa.

A cikin wannan sakon, Birgediya Janar Yousef al-Madani ya bayyana cikakken goyon bayan Yemen ga gwagwarmayar Falasdinawa, yana mai cewa: "Muna bin yarjejeniyar da alkawarin da muka yi muku. Muna tare da ku cikin farin ciki na nasara da kuma lokacin bakin ciki. Mun kuduri aniyar tsayawa tare da ku, ba tare da la'akari da girman sadaukarwar da za mu yi ba".

Ya yaba da aikin rundunar Qassam, yana mai cewa: "Kun nuna wa duniya babban misali na Tabbatuwar Musulunci kuma kun tabbatar da cewa Musulunci addini ne mai daraja da ba za a iya cin nasara a kansa ba. Wanda yake dauke da makamin imani, kun kayar da daular mai karfin dukiya, makamai, da fasaha.

Al-Madani ya kara da cewa: "Da karfin iradar kanku, kun ba wa duniya mamaki, kun sanya makiya yin shiru da juriyarku, kuma kun tilasta musu yin shawarwarin yarjejeniya, yayin da suke mafarkin mamaye ku da lalata ku".

A wani bangare na sakon, rundunar Qassam ta gode musu saboda ta'aziyyarsu kan shahadar Birgediya Janar Muhammad Abdul Karim Al-Ghamri. A cewar Al-Madani, wannan tausayin yana nuna zurfin alaƙar imani da jihadi tsakanin bangarorin biyu na gwagwarmayar fuskantar maƙiya Sahayoniya da kuma makircinsu na mugunta.

Abin lura ne cewa Sayyid Abdul-Malik Al-Houthi, shugaban ƙungiyar Ansarullah, ya yi kira da a shirya fuskantar gwamnatin Sahayoniya da ƙawayenta, yana mai jaddada cewa matuƙar mamayar yankin ta ci gaba, ba za a cimma kwanciyar hankali da tsaro ba.

………….

Your Comment

You are replying to: .
captcha